Mario Gotze ba zai sake wasa ba a bana

Mario Gotze a wasan Borussia Dortmund Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mario Gotze ya taimaka wa Bayern Munich ta dauki kofin Bundesliga uku, kuma shi ya ci wa Jamus kwallon da ta dauki Kofin Duniya na 2014

Mario Gotze ba zai sake wasa ba a bana yayin da yake cigaba da jinyar wata cuta da ta shafi kwayoyin halittarsa na ciki, amma ana sa ran zai warke sarai, ya taka leda a kakar wasa ta gaba, in ji kungiyarsa Dortmund.

Dan wasan, na Borussia Dortmund, mai shekara 24, wanda ya dauki Kofin Duniya da Jamus, a bana wasa tara kawai na gasar Bundesliga aka sa shi daga farko, saboda matsalar daurewar kafa da ya yi fama da ita, tun lokacin da ya je kungiyar daga Bayern Munich a bazarar da ta wuce.

Yanzu dai Gotze na karkashin wani shiri ne na musamman na kula da lafiyar tasa, kuma zai iya dawowa atisaye a farkon bazara mai zuwa, amma dai ana ganin hakan zai dogara ne ga yadda yake samun sauki in ji kungiyar ta Jamus.

Kungiyar ta ce babban burinta a kan dan wasan shi ne ya warke ta yadda zai dawo fagen wasa a kaka mai zuwa.

A wata sanarwa shugaban kungiyar ta Borussia Dortmund Hans-Joachim Watzke ya ce kungiyar da sunan magoya bayanta miliyan 10, tana yi wa dan wasan fatan samun sauki da wuri.

Gotze, wanda ya ci wa Jamus kwallon karin lokacin fitar da gwani a wasan karshe na cin Kofin Duniya na 2014, wasan minti 24 kawai ya yi a gasar Bundesliga a shekarar nan ta 2017.