An fitar da jadawalin gasar U-20 ta duniya

Diego Maradona na Argentina a wurin fitar da jadawalin Hakkin mallakar hoto JUNG YEON-JE /GETTY
Image caption Diego Maradona na Argentina ya halarci wajen hada jadawalin

An fitar da jadawalin gasar wasan kwallon kafa ta duniya ta matasa 'yan kasa da shekara 20 wadda za a yi a watan Mayu a Koriya ta Kudu.

Zakarun Afirka na matasan 'yan bal din, 'yan Zambia, wadanda a wasansu na farko za su hadu da Portugal wadda ta dauki kofin sau biyu, suna rukuni na uku ( Group C ), wanda ya hada da Iran da Costa Rica.

Guinea tana rukuni na daya ( Group A ), wanda ake ganin ya fi zafi, tare da mai masaukin baki, Koriya ta Kudu da Argentina wadda ta dauki kofin sau shida, da kuma tsoffin abokan hamayyarsu Ingila.

Afirka ta Kudu tana tare da Japan da Italiya da kuma Uruguay a rukuni na 4, ( Group D ),a wasan da za a fara daga 20 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Yuni.

Cikammakin wakilan Afirkan, Senegal tana rukuni na shida, ( Group F), tare da Ecuador da Amurka da Saudi Arabia.

Tsohon dan wasan Argentina wanda yana cikin tawagar kasarsa da ta dauki kofin na 1979, Diego Maradona, shi ne ya fito da sunayen kasashen yayin hada jadawalin, da kuma Pablo Aimar wanda shi kuma yake tawagar Argentinan da ta ci kofin a 1997.

An yi taron fitar da jadawalin ne a birnin Suwon na Koriya ta Kudu ranar Laraba.