Zaben Caf: Issa Hayatou na cikin matsi

Issa Hayatou Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Dadewar Issa Hayatou ke kara wa masu burin zabar Ahmad karfin guiwa

Nan da 'yan sa'o'i ne, a ranar Alhamis za a zabi shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, tsakanin dadadden shugaba mai ci Issa Hayatou da Ahmad na Madagascar.

A ranar Alhamis ne za a yi zaben a Ethiopia, wato Habasha, tsakanin shugaban na yanzu wanda ya yi shekara 29 yana jagorantar hukumar, Issa Hayatou, na kamaru, da kuma Ahmad na Madagascar.

Har a ranar Larabar ana can ana ci gaba da zawarcin kuri'un shugabannin hukumomin kwallon kafa na kasashen Afirka, yayin da suke shawarar wanda za su zaba tsakanin mutanen biyu.

Shugabanni biyar kawai Caf ta yi tun da aka kafa ta a shekara 60, kuma rabon da ta samu wani sabon shugaba tun 1988.

Zaben na ranar Alhamis na babban birnin Habasha, Addis Ababa, zai iya kawo sauyi, amma kuma Issa Hayatou, wanda a baya yawanci yake tsayawa takara ba mai kalubalantarsa bai sare ba.

A lokaci biyu da aka kalubalance shi, ya yi nasara da gagarumin rinjaye, inda shugabannin hukumomin kwallon kafa na Afirka suka ba shi cikakken goyon baya.

A shekara ta 2000, ya kayar da Armando Machado na Angola da kuria'a 47 da 4, kuma bayan shekara hudu ya doke Ismail Bhamjee na Botswana da kuri'a 46 da 6.

Yanzu kuma da yake neman wa'adinsa na takwas, inda yake takara da Ahmad na Madagascar, Hayatoun ya san cewa a wannan karon ba zai samu nasara cikin sauki ba.