Middlebrough ta kori kocinta Karanka

Aitor Karanka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A bara ne Karanka ya kai Middlebrough gasar Premier

Middlebrough ta kori kociyanta Aitor Karanka bayan shafe shekara uku da rabi a kungiyar, wadda a bara ta shigo Firimiya, amma kuma yanzu tana rukunin faduwa daga gasar.

kungiyar dai ba ta samu nasara a wasa 10 na firimiya da ta yi a baya bayan nan ba. kuma a yanzu tana cikin rukunin masu faduwa daga kasar, maki uku tsakaninta da tudun-mun-tsira, yayin da ya rage wasa 11 a kammala gasar

Haka kuma kungiyar ita ce mai karancin kwallaye a gasar inda ta zura 19 kawai, kuma a karshen makon da ya gabata ne, Manchester City ta fitar da ita daga gasar kofin FA.

Yanzu dai mataimakin kociyan, Steve Agnew ne zai jagoranci kungiyar.

Karanka mai shekara 43 ya gode wa kungiyar bisa damar da ta ba shi, tare da yaba wa duk wadanda ya yi aiki da su.

Tsohon mataimakin kociyan Real Madrid din, ya karbi aikin kungiyar ne a watan Nuwamban 2013, kuma shi ne kociyan kungiyar na farko wanda ba dan Burtaniya ba.

A bara ne kungiyar ta samu tsallakowa cikin gasar firimiya.

Tsohon kociyan Leicester Nigel Pearson ne na farkon wanda ake ganin zai samu damar gaje matsayin Karanka.