Ingila ta gayyaci Rashford da Defoe

Jermain Defoe na Sunderland Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jermain Defoe ya ci wa Sunderland kwallo 14 a Premier bana

Ingila ta sake gayyatar dan wasan gaba na Sunderland, Jermain Defoe, da Marcus Rashford na Manchester United, da kuma wasu sabbin 'yan wasa cikin tawagarta.

Dan wasan mai shekara 34 ya taka wa Ingila leda har sau 55, kuma wasan da ya yi mata na karshe shi ne wanda suka yi da kasar Chile a watan Nuwamban 2013.

Haka kuma 'yan wasa biyu na Southampton Nathan Redmond da James Ward-Prowse, wadanda ba su taba buga wa Ingila wasa ba, suma sun samu gayyatar, kamar dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford mai shekara 19.

Tawagar ta Gareth Southgate za ta ziyarci Jamus domin wasan gwaji da sada zumunta a ranar 22 ga watan Maris, kafin wasan da Ingilar za ta yi na neman gurbin Kofin Duniya da Lithuania a Wembley ranar 26 ga watan Maris.

Dan wasan tsakiya na West Brom Jake Livermore, wanda ya taba buga wa kasar sau daya, a lokacin karawarta da Italiya a 2012, shi ma na cikin tawagar.

Dan wasan baya na Burnley Michael Keane da dan wasan West Ham Michail Antonio su ne sauran wadanda ba su taba yi wa Ingila wasa ba, da suka samu gayyatar.

Shi ma Luke Shaw, wanda sau biyu kawai ya buga wa Manchester United wasa tun watan Disamba da kuma dan wasan tsakiya na Everton Ross Barkley, kociyan na Ingila ya gayyace su.