Europa: Man Utd za ta yi wasa ba Rooney da Martial

Wayne Rooney da Anthony Martial Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wayne Rooney da Anthony Martial ba za su yi wasan ba saboda rauni

Manchester United za ta yi wasanta na biyu na kofin Europa zagayen kungiyoyi 16 da FC Rostovt a Rasha a ranar Alhamis din nan ba tare da kyaftin dinta Wayne Rooney ba wanda ya ji rauni.

Haka shi ma Anthony Martial ba ya cikin tawagar, amma kuma Bafaranshe Luke Shaw da Bajamushe Bastian Schweinsteiger sun yi atisaye da wasu matasan 'yan wasan kungiyar, a gefe guda, a ranar Laraba.

Ita ma kungiyar FC Rostov ta Rasha za ta yi wasan na yau ba tare da kyaftin dinta ba Aleksandr Gatskan, wanda aka dakatar a wasan baya, da suka tashi kunnen-doki 1-1 a Rasha.

Duk kungiyar da ta dauki Kofin na Europa za ta samu gurbin gasar Zakarun Turai ta Uefa a kakar wasanni mai zuwa, wanda wannan wata dama ce mai kyau a wurin Man United, wadda take matsayi na shida a Premier.

Dan wasan tsakiya na Manchester United Marouane Fellaini ya ce kowa da kowa a kungiyar na cike da burin ganin sun je gasar ta Zakarun Turai ta Uefa a kaka mai zuwa, saboda haka za su yi iya kokarinsu na ganin burinsu ya cika.