Tennis : Federer ya doke Nadal, Kyrgios ya cinye Djokovic a gasar India

Roger Federer Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roger Federer ya dawo wasa ne a watan Janairu bayan jinyar wata shida

Roger Federer ya yi nasara kai tsaye a karo na uku akan Rafael Nadal, a karon farko a tarihinsa na wasan tennis na kwararru, kuma ya kai wasan dab da na kusa da karshe a babbar gasar tennis ta India.

Federer, dan Switzerland mai shekara 35, ya yi nasara da ci 6-2 6-3 , kamar yadda ya yi galaba a kan Nadal, dan Spaniya wata biyu da ya wuce, lokacin da ya dauki babban kofinsa na 18.

Yanzu a gaba zai kara da Nick Kyrgios dan Australia, wanda ya shammaci gwani na biyu a duniya Novak Djokovic da ci 6-4 7-6 (7-3).

A wasan mata da ake yi a gasar tennis din ta India kuwa, Svetlana Kuznetsova ta zama mace ta farko da ta kai wasan kusa da karshe a gasar.

'yar Rashan ta takwas a jerin gwanaye ta fitar da 'yar uwarta 'yar Rasha Anastasia Pavlyuchenkova da ci 6-3 6-2.

Da wannan nasara za ta hadu da 'yar gwana ta uku Karolina Pliskova 'yar Jamhuriyar Czech, wadda ita kuma ta fitar da Garbine Muguruza mai rike da kofin gasar Faransa, da ci 7-6 7-6.