Dole Lukaku ya mutunta kwantiraginsa da Everton - Koeman

Romelu Lukaku da kociyan Everton Ronald Koeman Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Romelu Lukaku ya yi watsi da tayin zama dan wasan kungiyar da ya fi daukar albashi a atrihi

Dole ne Romelu Lukaku ya mutunta kwantiraginsa da Everton duk da watsi da ya yi da tayin tsawaita zamansa da ba shi albashin da kungiyar ba ta taba biyan wani dan wasa ba a tarihi, in ji kocinsu Ronald Koeman.

A ranar Talata ne dan wasan gaban mai shekara 23 ya ce ba zai kulla wani sabon kwantira na shekara biyar da kungiyar ba, wanda za a rika biyansa fam dubu 140 a mako.

Dan wasan na Belgium yana tababa akan ko kungiyar ta Everton tana da irin burinsa na wasa a gasar Kofin Zakarun Turai na Uefa.

Kociyan ya ce idan da Everton ba kungiya ba ce da ke da buri mai yawa da bai rike ta ba.

Koeman ya ce kowa ya san abin da zai iya faruwa a wasan kwallon kafa, amma kana bukatar ka mutunta kwantiraginka.

Kociyan ya kara da cewa, shi ba shi da wata fargaba a kan lamarin saboda dan wasan yana da sauran sama da shekara biyu a kwantiraginsa.

Ya ce ba shi da wata matsala yanzu, saboda yana atisaye, kuma babu wani sauyi a dabi'arsa, sai dai kawai wasu 'yan abubuwa da ya furta, saboda haka ba bukatar a fitar da shi daga cikin 'yan wasan.