Man Utd ba za ta sake kaka-gida ba - Mourinho

Kociyan Manchester United Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jose Mourinho ya ce zamanin da Manchester United ta zama gagarabadau ya wuce

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce kungiyar ba ta da niyyar sake zama gagarabadau kuma ya kamata magoya bayanta su manta da tunanin za ta koma kamar zamanin Sir Alex Ferguson Ferguson.

A wata hira da BBC ta yi da kociyan ne, aka tambaye shi, ko zai iya dawo da kungiyar kamar da, sai dan Portugal din ya ce, a ma bar wannan magana.

Ya kara da cewa ka da ka yi kokarin komawa shekara 10 ko 20 baya, saboda ba abu ne da zai sake yuwuwa ba.

United ta dauki kofin Premier 13 a lokacin Alex Ferguson, amma kuma Mourinho ya ce ba abu ne mai yuwuwa ba ta sake irin wannan kaka-gida.

Kociyan ya ce Man United ba ta bukatar ta samu damar zuwa gasar Kofin Zakarun Turai kafin ta iya janyo manyan 'yan wasa.

Mourinho ya ce da shi ne yake kociyan Manchester a baya da ba zai sayar da Angel di Maria da Javier Hernandez da Danny Welbeck ba.

Sannan ya ce ba abu ne mai sauki ba ga dan wasansa na tsakiya Paul Pogba ya saba da salo da yanayin wasan Ingila ba.