Zakarun Turai: an fitar da jadawalin mataki na gaba

ECL Hakkin mallakar hoto .
Image caption Jadawalin matakin kusa da dab da na karshe a gasar zakarun Turai na bana

A ranar juma'a ne aka fitar da jadawalin matakin kusa da dab da na karshe na gasar zakarun Turai.

An hada Atletico Madrid da Leicester City yayin Borussia Dortmund za ta kara da Monaco.

Ita kuma Bayern Munich za ta fafata ne da Real Madrid inda Juventus za ta kece reni da Barcelona.

Za a yi zango na daya na wasannin ne tsakanin ranakun 11 da 12 na watan Afrilu.

Zango na biyu na wasannin kuma za a yi shi ne tsakanin ranakun 18 da 19 ga watan Afrilu.