Europa League: Man Utd za ta kara da Anderlecht

Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ibrahimovic na cikin fitattun 'yan wasan Manchester United

An hada Manchester United da zakarar gasar kwallon kafa ta Belgium, wato Anderlecht, a jadawalin matakin kusa da dab da na karshe na gasar cin kofin Europa.

United, wadda ake ganin za ta iya taka rawar gani a gasar, ce kungiyar Ingila tilo da take cikin gasar cin kofin Europar, wadda ke bin gasar zakarun Turai.

Kungiyar ta Jose Mourinho ta doke kungiuyar kwallon kafa ta Rasha, Rostov da 2-1 a zangon wasa biyu a mataki na baya.

Kungiyar kwallon kafa ta Lyon da ke Faransa za ta kara da Besiktas, yayinda Ajax za ta kece reni da Schalke ta Jamus, kuma Celta Vigo za ta hadu da Genk.

Za a buga wasannin zango na daya ne ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu.

Su kuma wasannin zango na biyun za a buga su ne mako daya bayan zango na farkon.