Man United ta ci wasanni 600 a gasar Premier

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption United ta koma matsayi na biyar a kan teburin Premier

Manchester United ta samu nasarar cin wasanni 600 a gasar Premier, bayan da ta doke Middlesbrough 3-1 a wasan mako na 29.

Hakan ya sa United ta zama kungiyar farko da ta kai wannan matakin na cin wasannin Premier a tarihi.

Wadanda suka ci wa United kwallayen sun hada da Marouane Fellaini da Jesse Lingard da kuma Luis Antonio Valencia, inda Boro ta zura kwallonta tilo ta hannun Rudy Gestede.

United din ta daga sama zuwa mataki na biyar a kan teburin Premier, bayan da ta yi kwanaki 184 a mataki na shida a gasar bana.

Haka kuma kungiyar da Jose Mourinho ke jagoranta ta buga wasanni 18 a jere a gasar ta Premier ba tare da an doke ta ba, tun rashin nasarar da ta yi a hannun Chelsea 4-0 a watan Oktoba.

Manchester United za ta karbi bakuncin West Brom a wasan da za ta buga na gaba a ranar 1 ga watan Afirilu a Old Trafford.

Labarai masu alaka