Kano Pillars ta doke Gombe United da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Kano Pillars ta ci Gombe United 2-0

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta doke Gombe United da ci 2-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 14 da suka fafata a ranar Lahadi.

Kano Pillars wadda ta karbi bakuncin Gombe a Kano, ta ci kwallayenta biyu ne ta hannun Najere.

A sauran wasanni bakwai din da aka fafata a yammacin Lahadin, Mountain Of Fire ta doke Plateau United 2-1, Wikki Tourist ma 2-1 ta ci Katsina United.

Karawa tsakanin Lobi Stars da Nasarawa United tashi suka yi babu ci, yayin da gumurzu tsakanin Abubakar Bukola Saraki da Enyimba suka yi kunnen doki 1-1.

Ga sakamakon wasannin da aka buga:

  • Tornadoes 1-0 Akwa
  • ABS 1-1 Enyimba
  • Wikki 2-1 Katsina
  • Lobi 0-0 Nasarawa
  • 3SC 0-0 Abia Warriors
  • FCIU 3-2 El-Kanemi
  • MFM 2-1 Plateau