FIFA ta dakatar da alkalin wasan Ghana

World Cup Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Afirka ta Kudu ce ta doke Senegal a wasan neman shiga gasar kofin duniya

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta haramta wa alkalin wasan Ghana jagorantar wasanninta har abada.

Fifa ta samu Joseph Lamptey da laifin cinikin wasanta na neman shiga gasar cin kofin duniya da aka yi a bara, tsakanin Afirka ta Kudu da Senegal.

A yayin karawar Lamptey ya bai wa Afirka ta Kudu fenariti, inda ya ce mai tsaron bayan Senegal, Kalidou Koulibaly, ya taba kwallo da hannu.

Fenaritin ya bai wa Afirka ta Kudu damar cin wasan da aka tashi da 2-1.

Amma da aka kalli fafatawar a faifan bidiyo, sai aka ga kwallon ta taba gwiwar kafar dan wasan ba hannunsa ba.

Lamptey zai iya daukaka kara a kan hukuncin a hukumar ta Fifa ko kuma a kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya.

Labarai masu alaka