Watakila Wenger ya ci gaba da zama a Arsenal

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wenger ya fara jan ragamar Arsenal tun a shekarar 1996

Arsenal ta karyata rade-radin cewar ta tuntubi kociyan Borussia Dortmund, Thomas Tuchel, domin ya maye gurbin Arsene Wenger.

A karshen kakar bana ne yarjejeniyar Wenger za ta kare a Emirates, sai dai kuma an yi masa tayin karin shekara biyu.

Wenger mai shekara 67 ya ce zai sanar da shawara kan makomarsa a kungiyar ta Arsenal.

Arsenal tana mataki na shida da maki 50 a kan teburin Premier, an kuma fitar da kungiyar daga gasar cin kofin zakarun Turai.

Sai dai kuma Gunners din ta kai wasan daf da karshe a gasar kofin FA, inda za ta fafata da Manchester City a ranar 23 ga watan Afirilu.