An tuhumi Man City da rashin da'a

Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan Man City da dama ne suka zagaye Michael Oliver a lokacin da ya bayar da fenareti

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Manchester City da nuna halin rashin da'a a lokacin da ta fafata da Liverpool a wasan Premier a ranar Lahadi.

City ta kasa tsawatar wa 'yan wasanta a lokacin da aka bai wa Liverpool bugun fenareti, bayan da Gael Clichy ya yi wa Roberto Firmino na Liverpool keta.

Milner ne ya buga fenaretin ya kuma ci kwallo daga baya ne Sergio Aguero ya farke, inda suka tashi kunnen doki 1-1.

Alkalin wasan Michael Oliver ya kuma bai wa Clichy da David Silver katin gargadi a lokacin da ya bayar da bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Hukumar ta bai wa Manchester City zuwa ranar 23 ga watan Maris domin ta kare kanta.

Labarai masu alaka