Abin da ya sa Schweinsteiger ya bar Man United

Bastian Schweinsteiger Hakkin mallakar hoto Reuters

Manchester United ta amince wa Bastian Schweinsteiger ya koma kungiyar Chicago Fire ta Amurka da taka-leda.

An cimma yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu ne a ranar Litinin, amma hakan zai tabbata ne idan dan kwallon ya tsallake gwajin lafiyar da za a yi masa.

Tsohon kyaftin din na Jamus, mai shekara 32, ya sanya hannu kan kwantiragin shekara daya, kamar yadda jaridar Chicago Tribune ta rawaito.

Ya ce, "Ina matukar bakin cikin rabuwa da abokanan wasana a United, sai dai ina godiya da kulob din ya bani damar murza-leda."

Ya kara da cewa: "Na ji dadin aiki tare da kocinmu, da 'yan wasa da kuma ma'aikatan kulob din, amma ina mika godiya ta musamman ga magoya bayan kungiyar... "

Schweinsteiger, wanda ya jagoranci Jamus ta samu nasara a gasar kofin duniya ta 2014, ya tattauna da Chicago Fire a bara, amma sai ya zabi ci gaba da zama a United har bayan kakar musayar 'yan wasan ta watan Janairu.

Chicago Fire sun nemi dan wasan ya fara aiki tare da su nan take, kuma ganin cewa ba ya cikin tsarin koci Jose Mourinho, United ta amince ya tafi.

Rashin jituwa da Mourinho na sahun gaba a cikin dalilan da suka sa shi barin United.

Labarai masu alaka