An yi barazanar kashe iyalina — Vardy

Jamie Vardy and Claudio Ranieri in discussion Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Vardy ya musanta rahotannin cewa yana da hannu a korar Claudio Ranieri

Jamie Vardy mai taka-leda a Leicester City ya ce an yi barazanar kashe iyalinsa da shi kansa tun bayan da kulob din ya kori Claudio Ranieri a matsayin koci.

Vardy, mai shekara 30, ya dora alhakin lamarin kan labaran karya da ke nuna cewa yana da hannu a matakin korar Ranieri.

A watan Fabrairu ne Ranieri ya raba-gari da kungiyar, wata tara bayan ya lashe gasar Premier, inda kulob din yake mataki na 17 a tebur.

Mutumin da ya gaje shi Craig Shakespeare, ya musanta cewa 'yan wasa sun yi wa kocin dan Italiya bore.

Vardy ya ce, "Wannan abin damuwa ne da takaici".

"Na karanta wani labari da ke cewa ina cikin wani taro da aka yi bayan wasanmu da Seville, bayan a zahiri ina wurin gwajin hukumar da ke kula da shan miyagun kwayoyi, inda na shafe sa'o'i uku".

"Amma sai ga shi jama'a na amfani da wannan suna kai wa iyalina hari."

Vardy ya ce ya yi kokari ya shawo kan lamarin, amma ya kara da cewa: "Amma akwai takaici idan ka ga mutane na kokarin kai wa matarka hari a lokacin da take tuka mota tare da yara, hakan bai dace ba."

Tun bayan tafiyar Ranieri, Leicester ta lashe wasa hudun da ta buga a jere, kuma a yanzu tana mataki na 15 a kan tebur.

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba