Za a buga El Clasico a watan Afirilu

El Clasico
Image caption Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a cikin watan Afirilu

Hukumar gudanar da gasar cin kofin La Liga ta Spaniya ta tsayar da ranar da za a kece raini tsakanin Real Madrid da Barcelona.

Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona ne a wasan mako na 33 a ranar 23 ga watan Afirilu a Santiago Bernabéu.

A watan Disamba kungiyoyin biyu sun tashi wasa kunnen doki a Camp Nou, inda Luis Suarez ya fara cin kwallo daga baya Sergio Ramos ya farke daf da za a tashi.

Madrid, wadda take ta daya a kan teburin La Liga, na fatan lashe kofin bana, wanda rabon ta da shi tun 2012 Barcelona ce ta biyu da tazarar maki biyu a teburin na La Liga.

Wasan da ake yi masa lakabi da El Clasico shi ne na karshe da kociyan Barcelona, Luis Enrique, zai kara da Madrid, bayan da ya sanar cewar zai bar Barca a karshen kakar bana.