Wa zai maye gurbin Enrique a Barcelona

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Enrique ya gaji aikin horar da Barcelona a wajen Gerardo Martino

A watan Maris kocin Barcelona, Luis Enrique, ya sanar da cewar zai yi murabus daga horar da kungiyar idan an kammala kakar bana.

Kocin ya ci karo da matsalolin da suka sa dole ya ajiye aiki, ciki har da rashin kokarin kungiyar da kasa walwalar Lionel Messi a filin wasa da sauransu.

Kafin karshen kakar wasan shekarar nan ake sa ran Barcelona za ta nada wanda zai maye Luis Enrique a Camp Nou.

Tuni dai aka fara hasashen cewa watakila kungiyar ta Spaniya ta zaba a cikin mutane biyu da suka hada da Juan Carlos Unzué ko kuma Ernesto Valverde.

Juan Carlos Unzué tsohon dan wasan Barcelona shi ne mataimakin Enrique ya kuma horar da Numancia da Racing Santander daga baya ya yi mataimaki a Celta, bayan nan ya koma mataimaki a Barca.

Shi kuwa Ernesto Valverde wanda ke jan ragamar Athletic Bilbao ya horar da Espanyol da Olympiacos da Villarreal da Olympiacos da Valencia ya kuma taka-leda a Barcelona.

Luis Enrique wanda ya fara aiki a Camp Nou daga watan Mayun 2014, ya ci kofunan La Liga biyu da Copa del Rey 2 da Supercopa na Spaniya da kofin zakarun Turai UEFA da UEFA Super Cup da kuma kofin zakarun nahiyoyi.