Ivory Coast ta nada Wilmots a matsayin kociyanta

Ivory Coast Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marc Wilmots tsohon dan wasan Belgium ya kai kasar gasar cin kofin duniya da gasar nahiyar Turai

Hukumar kwallon kafa ta Ivory Coast ta nada Marc Wilmots a matsayin sabon kociyan tawagar kwallon kafar kasar.

Wilmots mai shekara 48, ya horar da Belgium tsakanin 2012 zuwa 2016, inda ya kai kasar gasar cin kofin duniya.

Belgium ta raba-gari da kociyan, bayan da Wales ta doke ta 3-1 a gasar cin kofin zakarun Turai a watan Yulin 2016.

Wilmots ya maye gurbin Michel Dussuyer wanda ya yi ritaya, bayan da aka fitar da Ivory Coast daga gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Gabon a 2017.

Ivory Coast tana matsayi na daya da maki hudu a rukunin da ya hada da Gabon da Morocco da Mali.