Madrid za ta kara da Man City da United da Barca

International ChampionsCup Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A karshen kakar bana ne Madrid za ta fafata da Man United da City da kuma Barcelona a Amurka

Real Madrid za ta buga wasannin share fage a kasar Amurka a karshen kakar bana, domin samun damar lashe gasar International Champions Cup.

Wannan ita ce shekara ta biyar da Madrid din za ta yi wasannin a Amurka domin shirin tunkarar wasannin 2017/18.

Cikin fafatawar da Real Madrid din za ta yi har da karawa tsakaninta da Manchester United da Manchester City da kuma Barcelona.

Ga jerin wasannin da Madrid za ta yi a Amurka:

  • 23/7/2017 Manchester United a Santa Clara's Levi Stadium (California)
  • 26/7/2017 Manchester City a Los Angeles Memorial Coliseum stadium
  • 29/7/2017 Barcelona a Miami Hard Rock Stadium.