Watakila Sanchez da Ozil su bar Arsenal

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ozil ya koma Arsenal a shekarar 2013, inda Sanchez ya koma Gunners a 2014

Arsenal ta jingine tattaunawar da take yi da Alexis Sanchez da Mesut Ozil kan tsawaita musu yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a kungiyar, in ji Arsene Wenger.

Sauran shekara daya ta rage wa Sanchez da Ozil masu shekara 28, yarjejeniyarsu ta kare a Emirates.

Shi ma kociyan na Arsenal, Arsene Wenger bai saka hannu kan tayin shekara biyu da kungiyar ta yi masa ba, inda ya ce ya yanke shawarar makomarsa a Gunners.

Da aka tambaye shi kan batun makomar Sanchez sai ya ce "Har yanzu ba a cimma yarjejeniya da dan kwallon ba, kuma haka batun Ozil ma".

Wenger ya kara da cewar "duk dadewar da zan yi a Arsenal, zan ci gaba da jajircewa da kuma mayar da hankali a tsawon zaman da zan yi a Gunners.

Arsenal tana mataki na shida a kan teburin Premier, an kuma fitar da ita daga gasar cin kofin zakarun Turai na bana.

Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester City a gasar Premier a ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu a filin wasa na Emirates.

Labarai masu alaka