MFM ta haye teburin Firmiyar Nigeria

Nigerian Premier Eagle Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Mountain of Fire da El Kanemi da Kano Pillars sun ci wasanninsu bakwai da suka yi a gida

Kungiyar Mountain of Fire ta hau kan teburin gasar Firimiyar Nigeria, bayan da ta ci Rivers United 2-1 a kwantan wasan mako na takwas da suka kara a ranar Laraba.

Stephen Odey ne ya ci wa MFM kwallaye biyun, yayin da Rivers United ta zare kwallon daya ta hannun Christian Weli.

Da wannan sakamakon MFM ta zama ta daya a gasar Firimiyar Nigeria da maki 27 a wasanni 14 da ta yi, sai Plateau United ta biyu da maki 25, sai El Kanemi da maki 24.

A daya kwantan wasan mako na takwas kuwa, 3SC ce ta doke Enugu Rangers da ci daya mai ban haushi, inda Bode Daniel ne ya ci kwallon daf da za a tashi wasa.

Labarai masu alaka