Tawagar Ghana za ta kece-raini da ta Mexico

Ghana Black Stars Hakkin mallakar hoto GhanaFA
Image caption Ghana tana matsayi na uku a kan teburi a rukuni na biyar

Tawagar kwallon kafa ta Ghana za ta buga wasan sada zumunta da Mexico a ranar 28 ga watan Yuni a Amurka.

Black Stars wadda ke buga wasannin shiga gasar cin kofin duniya za ta kara da Mexico ne a filin wasa na Houston NRG.

Mexico ta ci Ghana a karawa biyu da suka yi a shekarar 2006 da kuma 2008, inda Guillermo Franco ne ya ci Black Stars daya mai ban haushi a wasan da suka yi a 2006.

Black Stars tana mataki na hudu a kan teburi a rukuni na biyar a wasannin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Tawagar kwallon kafa ta Mexico ta yi wasanni a filin NRG na Houstan sau 15, inda ta ci karawa bakwai, ta yi canjaras a wasanni shida aka doke ta sau biyu.

Labarai masu alaka