Odey ya ci kwallo 12 a Firimiyar Nigeria

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption An kammala wasannin mako na 14 a gasar Firimiyar Nijeriya

Bayan da aka buga wasannin mako na 14 a Gasar Firimiyar Nijeriya, Stephen Odey ne ke kan gaba a cin kwallaye.

Dan wasan na kungiyar Mountain of Fire (MFM) ya ci kwallo 12 jimilla, ciki har da guda biyun da ya ci Rivers United a kwantan wasan mako na takwas da suka tashi 2-1 a ranar Laraba.

Samuel Mathis na El-Kanemi, wanda ya ci kwallo bakwai ke rufa masa baya, sai Victor Mbaoma na Remo Stars da Mfon Udoh na Enyimba da kowannensu ya ci kwallo shida.

Kwallayen da Odey ya ci wa MFM sun sa kungiyar ta hau saman teburin gasar Firimiya da maki 27, sai Plateau United ta biyu da maki 25, yayin da El-Kanemi ke da maki 24 a mataki na uku.

A ranar 26 ga watan Maris ake sa ran ci gaba da wasannin mako na 15 a gasar cin kofin Firimiyar Nijeriya.

Labarai masu alaka