Everton za ta gina sabon filin wasa a Liverpool

Premier League Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun farko Everton ta so ta mallaki Walton Hall Park domin ta gina sabon filin wasan tamaula

Kungiyar Everton ta cimma yarjejeniyar mallakar wurin da za ta gina filin wasa da zai ci kudi fan miliyan 300 a birnin Liverpool.

Everton da Peel Holdings wadanda suka mallaki filin sun cimma matsaya ne a Branley Moore Dock kusa da River Mersey inda nan ne wurin da za a gina filin wasan.

A watan Fabrairu dan kasar Iran, Farhad Moshiri ya sayi kaso 49.9 ciki dari na hannun jarin kungiyar, kuma nan da nan ya fitar da tsare-tsaren barin Goodison Park mai cin 'yan kallo 39,572.

Tun farko Everton ta so ta mallaki Walton Hall Park domin ta gina sabon filin wasan tamaula, amma makwabtan wurin suka ki amincewa da shirin.

Haka kuma a baya kungiyar ta hakura da shirin da ta yi na koma wa King Dock a 2003 da kuma Kirkby a 2009.