Da kyar ne Sakho ya sake buga wasa a kakar bana

West Ham United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sakho ya yi rauni ne a cikin watan Nuwamba

Da wuya idan dan kwallon West Ham United, Diafra Sakho zai dawo buga wa kungiyar wasanni a bana, bayan da yake yin jinyar raunin da ya yi a bayansa tun cikin Nuwamba.

Wasanni biyu kacal Sakho ya buga wa West Ham a kakar shekarar nan, sakamakon ciwon baya da ya yi fama da shi.

Koda yake Sakho mai shekara 27 ya fara yin atisaye shi kadai, bayan da likitoci suka yi masa aiki.

Jami'in da ke kula da lafiyar 'yan wasan kungiyar Stijn Vandenbrouck ya ce idan dan wasa ya dawo daga jinya, yana bukatar makonni hudu zuwa biyar kafin ya dawo murza-leda cikin 'yan wasa.

Sakho dan kwallon tawagar Senegal wanda aka yi shirin zai koma West Brom kan kudi fam miliyan 15 kafin ya ji rauni, bai buga gasar kofin Afirka da aka yi a Gabon ba.