An gayyaci dan wasan Middlesbrough, Gibson cikin tawagar Ingila

Ben Gibson Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gibson ya buga wa kasar wasannin 'yan kasa da shekara 21 har sau 10

Dan wasan baya na Middlesbrough, Ben Gibson zai shiga tawagar Ingila a karon farko.

Dan kwallon, mai shekara 24, na cikin tawagar ta Gareth Southgate a karawar da za su yi da Lithuania, a wasan neman gurbin kofin duniya ranar Lahadi a Wembly.

Dan wasan bayan, ya samu shiga cikin tawagar ne, saboda raunin da dan wasan Manchester united, Chris Smalling ya ji.

Dan wasan na Manchester United dai ya koma Old Trafford, yayin da dan wasan Chealsea Gary Cahill ya bar sansanin horon, bayan da aka dakatar da shi daga wasan.

Gibson din dai, zai samo sauran 'yan tawagar a sansanin karbar horo, ranar Juma'a da yamma, kuma zai karbi horo tare da su, ranar Asabar da yamma.

A wasansa na farko a matsayin cikakken kocin Ingila, Southgate ya yi rashin nasara a hannun Jamus da ci 1-0, a wasan sada zumunci da suka buga ranar Laraba da yamma a Dortmund.

Za su yi wasansu na ranar Lahadi ne, yayin da ba a doke su ba, kuma su ne na daya a rukunin F da maki 10.

Labarai masu alaka