Wasanni tara Madrid za ta yi a watan Afirilu

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Madrid ce ke mataki na daya a kan teburin La Liga

Da zarar an kammala wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya ne ake sa ran ci gaba da buga wasannin League a karshen mako a nahiyar Turai.

A karshen makon ne za a fara barje-gumi tsakanin kungiyoyin da suka buga tamaula a cikin watan Afirilu da suka hada da gasar Premier da ta Spaniya Bundesliga da Serie A da sauransu.

Real Madrid wadda ke kan teburin gasar La Liga za ta yi wasanni tara a cikin watan gobe, inda za ta fara karbar bakuncin Alaves a wasan mako na 29 a ranar Lahadi.

A ranar Laraba kuwa Madrid din za ta ziyarci Leganes a karawar mako na 30, sannan ta karbi bakuncin Atletico a wasan mako na 31 a ranar Asabar.

Daga nan ne Real Madrid za ta ziyarci Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai sannan ta ziyarci Sporting a wasan La Liga mako na 32.

A gasar La Liga mako na 33 neReal Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a El Clasico a cikin watan Afirilu sannan ta ziyarci Deportivo ta kuma sauki Valencia a Bernebue.

Ga jerin wasannin da Real Madrid za ta yi a cikin watan Afirilu:

  • LaLiga (mako 29) Real Madrid-Alavés
  • LaLiga (maako 30) Leganés-Real Madrid
  • LaLiga (mako 31) Real Madrid-Atlético
  • Gasar zakarun Turai Bayern-Real Madrid
  • LaLiga (mako na 32) Sporting-Real Madrid Saturday
  • Gasar zakarun Turai Real Madrid-Bayern
  • LaLiga (mako na 33) Real Madrid-Barcelona
  • LaLiga (mako na 34) Deportivo-Real Madrid
  • LaLiga (mako na 35) Real Madrid-Valencia

.

Labarai masu alaka