Mai Takwasara ya dambata da Shagon Dan Digiri

Damben gargajiya
Image caption Turmi biyu suka dambata a tsakaninsu babu kisa aka raba su.

An ci gaba da wasannin damben gargajiya da kungiya ta kasa ta shirya wa Ali Zuma ajo, wanda aka fara tun daga ranar Juma'a da yammaci.

Da safiyar Lahadi aka ci gaba da wasannin dambe, inda aka fafata da dama ciki har da karawa tsakanin Dogo Mai Takwasara daga Guramada da Shagon Dan Digiri daga Kudu.

'Yan wasan sun yi turmi biyu babu kisa aka raba su a dambatawar da suka yi a filin wasa da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Da yammacin Lahadi ake sa ran yi wa Ali Zuma ajo domin sada zumunta tsakanin mambobin kungiyar damben gargajiya ta kasa.

Daga nan ne kuma za su gudanar da taro domin tsayar da rana da za a yi wasan damben gargajiya na kasa da za a yi a jihar Niger ta Nigeria.

Labarai masu alaka