Federer ya fara gasar Miami Open da kafar dama

Roger Federer Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Federer ya lashe kofin Miami Open na biyu a 2006

Roger Federer ya fara gasar Miami Open da kafar dama, bayan da ya yi nasarar doke Frances Tiafoe a wasansa na farko a gasar tun bayan shekara uku.

Federer mai shekara 35 ya fitar da Tiafoe mai shekara 19 da ci 7-6 (7-2) 6-3, inda hakan ya sa ya ci wasanni 14, aka doke shi a karawa daya a kakar kwallon tennis ta 2017.

Dan kasar Switzerland wanda ya lashe kofin Australian Open da Indian Wells a bana, bai halarci gasar Miami Open ta 2016 ba, sakamakon rashin lafiya da ya yi fama.

Wasu daga sakamakon wasannin da aka yi Stan Wawrinka ya doke Horacio Zeballos da ci 6-3 6-4, yayin da Agnieszka Radwanska ta yi rashin nasara a hannun Mirjana Lucic-Baroni da ci 6-0 6-3.