Barcelona za ta karrama Johan Cruyff

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Johan Crufff tsohon dan wasan Barcelona wanda ya kuma horar da ita tamaula

Kungiyar Barcelona za ta yi mutun-mutumin tsohon dan wasanta wanda ya horar da ita tamaula Johan Cruyff a filinta na Nou Camp.

Haka kuma kungiyar za ta gina katafaren wuri don matasan kungiyar da ke murza mata leda da za ta saka sunan marigayin dan kasar Netherlands.

Barcelona ta sanar da wannan shirin kwana daya da aka yi bikin tunawa da cikarsa shekaa daya da mutuwa, yana da shekara 68.

Cruyff ya lashe kofuna 13 a matsayin dan wasa da lokacin da ya jagoranci Barcelona, ciki har da kofin zakarun Turai na 1992.

Labarai masu alaka