Ingila ta fara jin kanshin gasar kofin duniya ta Rasha

World Cup Qualifier
Image caption Dan wasan Sunderland Jermain Defoe ne ya fara ci wa Ingila kwallon farko, Jamie Vardy ya ci ta biyu

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta doke ta Luthuania da ci 2-0 a wasa na biyar a cikin rukuni na shida a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da suka yi a ranar Lahadi.

Dan wasan Sunderland, Jermain Defoe wanda rabonsa da buga wa Ingila tamaula tun 2013 ne, ya fara cin kwallo a minti na 21 da fara tamaula.

Sai da aka dawo ne daga hutu Jamie Vardy mai murza-leda a Leicester City ya ci ta biyu, bayan da ya samu tamaula daga wajen Adam Lalana.

Bayan da aka yi wasanni biyar-biyar a rukuni na shida, Ingila ce kan gaba a kan teburi da maki 13, Slovenia ce ta biyu mai maki 9, sai Slovakia biye da ita da maki 7.

Wasu sakamakon wasannin da aka yi:

  • Azerbaijan 1-4 Jamus
  • San Marino 0-6 Jamhuriyar Czech
  • Armenia 2 Kazakhstan 0