Abia ta samu maki uku a kan Kano Pillars

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Abia Warriors ta ci Kano Pillars a wasan gasar mako na 15 a Firimiyar Nigeria

Kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors ta ci Kano Pillars 3-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako 15 da suka fafata a ranar Lahadi.

Kano Pillars ce ta fara cin gida ta hannun dan wasanta Joel Djondang a minti na takwas, Sherif Bashir ne ya ci Pillars kwallo na biyu bayan da aka dawo daga hutu.

Ba a dauki lokaci tsakanin kwallo na biyu da aka ci Pillars ba, Sunday Adetunji ya kara ta uku a raga.

  • Ga sauran sakamakon wasannin mako na 15:
  • Katsina 1-0 Rangers
  • Remo 2-1 Wikki
  • Enyimba 1-0 Rivers
  • Plateau 4-1 ABS
  • Gombe 1-0 MFM FC
  • Nasarawa 1-0 3SC
  • Tornadoes 2-1 Sunshine
  • El-Kanemi 1-0 Lobi

Labarai masu alaka