Netherlands ta raba gari da Danny Blind

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Danny Blind ya ci wasanni 7 daga 17 da ya yi tun lokacin da ya karbi aiki a 2015

Hukumar kwallon kafa ta Netherlands ta kori kociyan tawagar kwallon kafar kasar Danny Blind, bayan da ya yi shekara biyu yana aikin.

Netherland ta sallami kociyan ne sakamakon doke ta 2-0 da Bulgariya ta yi a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a ranar Asabar.

Kuma rashin nasarar da kasar ta yi ya sa tana mataki na hudu a rukunin farko bayan da suka yi wasanni biyar-biyar.

Blind mai shekara 55, ya karbi aikin horar da Netherlands a wurin Guus Hiddink a shekarar 2015, inda ya kasa kai kasar gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a Faransa.

An bai wa Fred Grim rikon kwarya, inda zai ja ragamar kasar a wasan da za ta buga da Italiya a ranar Talata.

Labarai masu alaka