Barcelona ta ci wasa 799 a Camp Nou

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona tana matsayi na biyu da maki 63 a kan teburin La Liga

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, wadda ke mataki na biyu a kan teburin La Liga, ta ci wasannin gasar sau 799 a filin wasanta na Camp Nou.

Barcelona ta buga wasannin La Liga 1,056 a gida jimilla, inda ta lashe karawa 799, ta yi rashin nasara a fafatawa 164 aka doke ta sau 93.

Haka kuma kungiyar ta Spaniya ta fafata sau 1,515 a dukkan karawar da ta yi a gida ciki har da gasar cin Kofin Zakarun Turai da Europa Cup da wasannin gasar Spaniya da sauransu.

Jimilla Barcelona ta yi nasarar cin wasanni 1,131 a karawar da ta yi a Camp Nou, ta yi canjaras sau 241 aka doke ta sau 143.

A ranar Asabar ne Granada za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na 29 a gasar La Liga, kafin kungiyar ta kece-raini da Sevilla a wasan mako na 30 a ranar Laraba 5 ga watan Afirilu a Camp Nou.

Labarai masu alaka