An ci kwallo 274 a gasar Firimiyar Nigeria

Nigerian Premier League Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption A ranar Lahadi aka buga wasannin mako na 15 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Kwallaye 274 aka zura a raga a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka buga wasanni 144 a karshen mako.

A ranar Lahadi aka yi wasannin mako na 15, inda aka ci kwallaye 22, kuma karawar da aka yi tsakanin Akwa United da Ifeanyi Ubah ce aka tashi kunnen doki, sauran wasannin kungiyoyin da suke gida ne suka yi nasara.

A ranar ta Lahadi, wasan da Plateau United ta doke Abubakar Bukola Saraki 4-1 shi ne wanda aka fi cin kwallaye, sai wanda Abia Warriors ta ci Kano Pillars 3-0.

Bayan da aka yi wasanni goma a ranar Lahadin, Plateau United ce ta daya a kan teburi da maki 28, sai Mountain of Fire ta byu da maki 27, ita ma El-Kanemi Warriors maki 27 ne da ita.

Labarai masu alaka