Ba na son batun mutuwar matata - Ferdinand

England
Image caption Tsohon kyaftin din Manchester United da tawagar kwallon kafa ta Ingila

Tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ingila, Rio Ferdinand, ya shaida wa BBC cewar 'ya yansa ba za su tattauna kan batun mutuwar mahaifiyarsu ba.

Ferdinand, tsohon dan wasan Manchester United, ya ce yaran nasa kan sa jikin shi ya yi sanyi, idan ya tambaye su yadda suke ji kan rashin mahaifiyarsu.

Ya kara da cewar bai san ranar da zai gana da yaran uku masu shekara 10 da takwas da kuma biyar kan mutuwar mahaifiyar tasu.

Rebecca, wadda Ferdinand ya aura a shekarar 2009, ta mutu tana da shekara 34 sakamakon sankarar mama a watan Mayun 2015.

Ya kuma ce har yanzu bai san me zai ce musu ba dangane da rashin matarsa da ya yi, bai kuma san dabarar da zai yi musu don sanar da su ba.

Labarai masu alaka