Hukumar FA ta ci tarar Man City fam 35,000

Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan Man City da dama ne suka zagaye Michael Oliver a lokacin da ya bayar da fenareti

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar Manchester City fam 35,000, bayan da ta same ta da halin rashin da'a a lokacin da ta fafata da Liverpool a wasan Premier.

City ta kasa tsawatar wa 'yan wasanta a lokacin da aka bai wa Liverpool bugun fenareti, bayan da Gael Clichy ya yi wa Roberto Firmino na Liverpool keta.

Milner ne ya buga fenaretin ya kuma ci kwallo, daga baya ne Sergio Aguero ya farke, inda suka tashi kunnen doki 1-1.

Alkalin wasan Michael Oliver ya kuma bai wa Clichy da David Silver katin gargadi a lokacin da ya bayar da bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Labarai masu alaka