Zan yi ruwan kwallaye a Indonesia — Odemwingie

Tsohon dan wasan gaba na Najeriya Peter Odemwingie Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon dan wasan gaba na Najeriya Peter Odemwingie, na fatan cin kwallaye da maimaita irin nasarar da ya samu a baya, a sabon kulob dinsa na Madura United da ke Indonesia.

Dan kwallon mai shekara 35, wanda ya wakilci Super Eagles a gasar cin kofin duniya ta 2010 da 2014, ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara guda tare da zabin tsawaita wa.

Rabon Odemwingie da kulob tun watan Janairu lokacin da ya bar kungiyar Rotherham ta Ingila.

Ya shaida wa BBC cewa: "Wannan lokaci ne mai kayatarwa ga harkar kwallon kafa a Indonesia, kuma na yi farin cikin kasance wa a nan".

"Ina fatan zan samu irin nasarorin da na samu a shekarun da suka gabata ta hanyar cin kwallaye masu amfani ga Madura."

Ya zamo tsohon dan wasan Premier na uku da ya koma Indonesia bayan Michael Essien da Carlton Cole.

Odemwingie ya kara da cewa, "Ban san komai game da wannan kasar ba amma na samu shawarwari masu kyau daga Michael Essien".

Dan wasan, wanda haifaffen Uzbekistan ne, ya kuma taka leda a Belgium, Faransa da Rasha kafin ya shafe shekara bakwan da ta gabata a Ingila, inda ya buga wasa a West Bromwich Albion da Stoke City.

Labarai masu alaka