Zuwa gasar Turai na da matukar wuya - Wenger

Arsenal manager Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wenger bai taba kasa zuwa gasar zakarun Turai ba tun da ya zo Arsenal a 1996

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce halin da kulob din ya samu kansa a ciki ya nuna cewa zuwa gasar zakarun Turai a yanzu ba abu ne mai sauki ba kamar yadda yake a baya.

Wenger ya jagoranci Gunners zuwa gasar shekera 20 a jere.

Sai dai a yayin da ya rage saura wasa 10 a kammala kakar bana, suna mataki na shida da tazarar maki bakwai tsakaninsu da kungiyar da ke mataki na hudu.

Ya ce: "Abu ne mai wahala sai dai ina ganin zai yi wu".

"Na shafe shekara 20 ina yi kuma kamar babu wahala. Amma kwatsam, sai ya zamo abin da ya zamo, kuma ina farin ciki cewa mutane sun gane ba abu ne mai sauki ba kamar a da ba."

A shekarar 2012 Wenger ya kwatanta kare wa a mataki na hudun farko da lashe kofi, kuma a kwanan nan kocin Manchester City ya maimaita hakan.

Ya kara da cewa "Idan kuka saurari Guardiola, ya fada kwanaki cewa kammala gasar lig a mataki na hudun farko a Ingila tamkar lashe kofi ne saboda yana da matukar wahala".

Wenger ya kuma sake yin watsi da rade-radin da ake yi kan makomarsa da kuma ta Alexis Sanchez a kungiyar.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba