Fifa ta dakatar da Lionel Messi da cin tara

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Messi ba zai buga wa Argentina wasanni hudu ba, sannan zai biya tarar kudi

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta dakatar da Lionel Messi daga buga wa tawagar kwallon kafa ta Argentina wasa hudu.

Fifa ta hukunta dan wasan da ke taka-leda a Barcelona ne sakamakon samunsa da laifin yin kalaman cin mutunci ga mataimakin alkalin wasa a karawar da Argentina ta ci Chile 1-0.

Messi, wanda shi ne ya ci kwallo a fafatawar ta neman shiga gasar cin kofin duniya, ya yi fushi a lokacin da aka hura ya yi laifi, inda ya dinga yi wa mataimakin alkalin wasa surutai.

Haka kuma hukumar ta Fifa ta ci tarar Messi mai shekara 29 kudi fan 8,100.

Argentina tana mataki na uku a teburin wasannin shiga gasar cin kofin duniya a Kudancin Amurka, kuma saura wasanni biyar suka rage.

Kasashe biyar ne za su wakilci nahiyar a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2017.

Labarai masu alaka