An cire takunkumin da aka saka wa Partizan

Partizan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Partizan ta taba kai wa wasan karshe a kofin zakarun Turai a 1966

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta ce ta cire takunkumin da ta saka wa Partizan Belgrade, bayan da kungiyar ta biya bashin da ake bin ta.

Hukumar ta samu kungiyar da ke buga gasar Serbia da laifin kin biyan bashin kakar wasa uku a cikin shekara biyar.

Tuni kotun da ke kula da kararrakin wasanni ta duniya ta ce Partizan ta nuna mata shaidar takardun bashin da ta biya wanda hukumar kwallon kafar Turai ke bin ta.

Hakan kuma na nufin FK Partizan ta can-can-ci shiga wasannin cin kofin zakarun kungiyoyin Turai.

Labarai masu alaka