An yi gobara a filin wasa na Shanghai Shenhua

China League Hakkin mallakar hoto Shanghai Shenhua
Image caption A cikin watan nan ake sa ran fara gasar cin kofin kasar China

Wani bangare a katafaren filin wasan kwallon kafa na Hongkou na kungiyar Shanghai Shenhua ya lalace sakamakon gobara.

Babu wanda ya ji rauni ko hasarar rai a hadarin da ya faru da safiyar Talata.

Wani rahoto ya ce gobarar ba ta shafi warin zaman 'yan kallo ko filin wasa ba, amma ana binciken musabbabinta.

A cikin watan nan ake sa ran fara gasar cin kofin kasar China, inda Shenhua za ta karbi bakuncin Changchun Yatai a wasan farko da za ta yi a gida a ranar 16 ga watan Afirilu.

Kungiyar wadda Gus Poyet ke jagoranta ita ce ta sayo tsohon dan kwallon Manchester City, Carlos Tevez a bara kan kudi fam miliyan 40.

Labarai masu alaka