Brazil ta zama ta farko da ta kai gasar kofin duniya

Brazil Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Brazil ta zama ta farko da ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za ayi a Rasha a 2018

Tawagar kwallon kafa ta Brazil, ta zama ta farko da ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Nasarar da Brazil ta doke Paraguay 3-0, da cin Argentina da Uruguay da aka yi ne, ya bai wa kasar damar ci gaba da zama ta daya a kan teburin Kudancin Amurka.

Brazil ta ci kwallayenta uku ta hannun Philippe Coutinho mai wasa a Liverpool da Neymar mai taka-leda a Barcelona da Marcelo mai murza-leda a Real Madrid.

A karawar sai da Neymar ya barar da fenareti, kuma nasarar da Brazil ta yi ya sa ta bai wa Colombia wadda ke mataki na biyu a kan teburi tazarar maki tara.

Wannan ne karo na takwas da Brazil ta lashe wasanni a jere a karkashin koci Tite.

Argentina wadda ta lashe kofin duniya sau biyu tana matsayi na biyar, bayan da Bolivia ta doke ta 2-0.

Labarai masu alaka