Dan wasan Kenya ya shigar da korafi a Fifa

Kenya National Team
Image caption Miheso ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Kenya wasa 14 ya kuma ci mata kwallo biyar

Dan wasan kasar Kenya, Clifton Miheso, ya shigar da korafi a Fifa, inda yake zargin an saka masa bakin bindiga domin ya katse yarjejeniyar buga wa Golden Arrows tamaula.

Miheso ya yi zargin cewar lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Janairu a ofishin kungiyar da ke birnin Durban a Afirka ta Kudu.

Dan wasan mai shekara 24 na son a dakatar da shirin sayar da shi ga wata kungiya, ko kuma a saka wa Golden Arrow takunkumi.

Haka kuma ya bukaci kungiyar ta biya shi kudi dala 22,000 albashin da yake bi bashi.

Golden Arrow ta musanta zargin da dan kwallon ke yi mata, kuma tun daga lokacin ta ki cewa komai kan lamarin.

Miheso ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Kenya wasa 14 ya kuma ci mata kwallo biyar.

Labarai masu alaka