Lamela ya gama buga wasannin bana

Tottenham Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Erik Lamela ya ci kwallaye biyu a wasanni 14 da ya buga wa Tottenham

Dan kwallon Tottenham, Erik Lamela, ya gama buga wasannin kakar bana, sakamakon raunin da ya yi.

Dan kwallon mai shekara 25 dan kasar Argentina, bai buga wa Tottenham wasa ba tun cikin watan Oktoba, sakamakon raunin da ake sa ran likitoci za su yi masa aiki a ranar Asabar.

Lamela ya yi wasanni 14 a Tottenham a kakar shekarar nan, kafin ya yi rauni.

Dan kwallon ya koma Spurs daga Roma a 2013, inda ya ci wa kungiyar kwallaye 13 a bara.