Pillars da Nasarawa United sun raba maki

Nigerian Premier League
Image caption Wasanni tara aka buga a ranar Laraba a gasar cin kofin Firimiyar Nigera

Kungiyar Kano Pillars ta tashi wasa kunnen doki 1-1 tsakanin ta da Nasarawa United a wasan mako na 16 a gasar Firimiyar Nigeria da suka yi a ranar Laraba.

Pillars ce ta fara cin kwallo ta hannun Mubarak Said a minti na tara da fara tamaula, yayin da Nasarawa United ta farke ta hannun Adamu Hassan bayan da aka dawo daga hutu.

Sai a ranar Alhamis Lobi Stars za ta karbi bakuncin Akwa United.

Ga sakamakon wasanni tara da aka buga a ranar Laraba:

  • Rangers 1-1 Remo
  • Wikki 1-0 Enyimba
  • Rivers 0-0 Plateau
  • ABS 1-1 Gombe
  • MFM 2-1 Abia Warriors
  • 3SC 1-0 El-Kanemi
  • FCIU 1-0 Tornadoes
  • Sunshine 2-0 Katsina

Labarai masu alaka