Kungiyar Manchester City ta mata, ta kai wasan kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption 'Yan wasan Manchester City na murnar nasarar da suka samu

Kungiyar Manchester City ta mata, ta zama kungiyar Ingila ta farko da ta samu zuwa wasan kusa da karshe, a gasar zakarun turai tun shekarar 2014 bayan doke Fortuna Hjorring da ci 2-0, jumulla gida da waje.

Lucy Bronze ce ta sanya kungiyar ta city a gaba bayan da ta zura kwallo da ka, a ragar Fortuna Hjorring, tun a zagaye na farko na wasan.

Zakarun na super leage,sun doke kungiyar ta Denmark da ci 1-0 a wasan farko sannan kuma suka kara kare matsayinsu ta hanyar kwallon da Lucy Bronze ta zura.

City dai za ta kara da Lyon a wasan kusa da karshe da za su fafata, a nan gaba cikin watan Afrilu.

Lyon wacce ke rike da kofin, ta samu zuwa wannan matakin ne bayan da ta samu nasara a kan Wolfsburg, da ci 2-1 jumulla gida da waje, wani wasan na kusa da karshe da za a yi, shi ne tsakanin Barcelona da Paris St-Germain.

Za a yi wasannin dai a ranakun 22 da 23 ga watan Afrilu, A yayin da za a yi wasan karshe a filin wasa na Cardiff City ranar daya ga watan Yuni.

Tun dai shekarar 2014 rabon da kungiyar mata ta Manchester City, ta dauki kofi, sai dai kuma yanzu kungiyar na da damar daukar kofuna biyar a kasa da watanni tara.

Yanzu haka dai kungiyar ta samu nasarar daukar kofin WSL, da kofin Nahiyoyi, kuma yanzu haka sun kai matakin wasan kusa da karshe a kofin FA.

Labarai masu alaka